Tilasta dalibai yin lalata: 'Yan sanda sun cafke malamin jami'a, jami'a ta dakatar da shi

Tilasta dalibai yin lalata: 'Yan sanda sun cafke malamin jami'a, jami'a ta dakatar da shi

Wani malamin jami'a, Mista Kisuze Edward, ya shiga hannun jami'an 'yan sanda bayan jami'ar da yake koyarwa ta dakatar da shi daga aiki.

A takardar dakatarwar da jami'ar ta buga kuma ta saka a shafin ta na Tuwita a yau, jami'ar ta ce ta dakatar da malamin ne bisa zargin kokarin tilasta wata daliba yin lalata kamar yadda ta shigar da korafi gaban hukumar jami'ar.

Hukumar jami'ar ta bawa malamin damar kare kan sa bayan karbar korafin dalibar.

Tilasta dalibai yin lalata: 'Yan sanda sun cafke malamin jami'a, jami'a ta dakatar da shi

Tilasta dalibai yin lalata: 'Yan sanda sun cafke malamin jami'a, jami'a ta dakatar da shi

Bayan mika na sa rahoton ne sai hukumar jami'ar ta dakatar da shi tare da cigaba da biyan sa rabin albashi har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

DUBA WANNAN: Duba Jerin sunayen mutanen da suka shiga majalisar dattijai suka sace sandar majalisa

A wani rahoton mai alaka da wannan, ana cigaba da cece-kuce a kan wani sautin murya da wata dalibar jami'ar OAU Ife ta yada inda wani Farfesa ya nemi ya kwanta da ita sau biyar ko kuma ya kayar da ita jarrabawa.

Babu rahoton ya zuwa yanzu jami'ar ta dakatar da malamin ko kuma ta dauki wani mataki a kan sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel