Siyasa: Dalilan da zasu sa a tsige shugaba Buhari, mulkinsa ya saba qa'ida - Aborisade

Siyasa: Dalilan da zasu sa a tsige shugaba Buhari, mulkinsa ya saba qa'ida - Aborisade

- Shugaba Buhari yana ganin soyayya da kuma baqar kiyayya

- Zai ci gaba da ganinta, musamman bayan da ya ayyana sake son tsayawa takara 2019

- Borisade n ganin kamata yayi a tsige shi tun yanzu, kafin ya zarce

Siyasa: Dalilan da zasu sa a tsige shugaba Buhari, mulkinsa ya saba qa'ida - Aborisade

Siyasa: Dalilan da zasu sa a tsige shugaba Buhari, mulkinsa ya saba qa'ida - Aborisade

Buhari ya rasa damar shugabantar mu kamar yanda kundin tsarin mulki ya nuna- a tsige shi inji Aborisade.

Aborisade yace haka lokacin da yake maida martanin sakamakon harin da aka kaiwa 'yan shi'a kwanan nan a zanga zangar da sukayi don sakin shugaban su, Ibrahim El-Zakzaky a Abuja.

Lauya kuma mai kare hakkin 'Dan Adam Mista Femi Aborisade yace shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dace da ya cigaba da shugabantar kasar ba kuma majalisar dattawa tayi gaggawar tsige shi.

Aborisade ya kalubalanci ' yan sandan da suka kai harin ga 'yan Najeriya masu zanga zangar lumana ba tare da makamai ba.

"Ina kushe abinda jami'an tsaro sukayi wa ' yan shi'a a ranar 16 ga watan Afirilu 2018. Wanda yayi sakamakon mutuwar wasu da kuma munanan raunika da yawancin masu zanga zangar suka samu."

Yace tarwatsa masu zanga zangar lumana ba kamata ba karkashin mulkin farar hula da kuma gwamnatin damokaradiyya, kari da cewa APC da kuma Gwamnatin Buhari sun cigaba da nuna basu mutunta dokar kotu da ta bada umarnin sakin Ibrahim El-Zakzaky da matar shi da suke tsare.

DUBA WANNAN: An saki wani bidiyo da bai yi wa Buhari dadi ba

Mai kare hakkin yace dole ne Shugaban kasar ya hukunta wanda ya bada umarnin tarwatsa 'yan shi'a, in ba haka ba majalisar dattawa su fara shirin tsige shi.

Yayi kira da a hanzarta sakin El-Zakzaky, matar shi da kuma duk wadanda ke tsare sakamakon zanga zangar lumana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel