Fayose yayi Allah-wadai da abin da ya auku a Majalisar Dattawa

Fayose yayi Allah-wadai da abin da ya auku a Majalisar Dattawa

- Gwamna Ayo Fayose yace Shugaban kasa ya daurewa Sanata Agege gindi

- Dazu Sanatan na APC da aka dakatar ya shiga cikin Majalisa da tsageru

- Ayo Fayose yace Shugaba Buhari ya goyi baya aka yi wannan danyen aiki

A yau ne Majalisar Dattawa ta shiga cikin hatsaniya bayan da wani Sanatan Kudancin kasar na Jam’iyyar APC mai mulki da aka dakatar ya fado cikin Majalisar ya kuma tada rikici ana zama.

Fayose yayi Allah-wadai da abin da ya auku a Majalisar Dattawa

Gwamna Fayose yace Sanata Agege yayi abin kunya

Sanata Omo-Agege ya dauke sandar girman Majalisar kasar wanda hakan ya jawo aka aiko Jami’an tsaro cikin Majalisa. Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ta shafin sa na Tuwita yayi tir da wannan abu da ya faru a Majalisar.

KU KARANTA: Harin da aka kai a Majalisar Dattawa ta'addanci ne - Majalisar Wakilai

Gwamnan da ke adawa da Gwamnatin Shugaba Buhari yace Sanatan da yayi wannan abin kunya ya samu daurin-gindi ne daga Shugaban kasa. Ayo Fayose ya kuma nemi a dauki tsattsauran mataki game da wannan danyen aiki.

Wannan ne karo na farko da aka samu tsageru sun shiga har cikin Majalisar Dattawan Kasar sun yi gaba da sandar girma tun da aka dawo siyasa a 1999 inji Gwamnan na Ekiti. A dalilin haka dai sai da ‘Yan Sanda su ka shigo Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel