An kara samun wanda zai yi takarar kujeran Sanatan Bauchi da ya rasu

An kara samun wanda zai yi takarar kujeran Sanatan Bauchi da ya rasu

- Wani rikakken marubuci a Najeriya ya fito takarar Sanatan Bauchi

- Aliyu Tilde yana harin kujerar Marigayi Sanata A. Wakili da ya rasu

- Idan abubuwa sun tafi daidai Tilde zai yi takara ne a Jam’iyyar NNPP

Jam’iyyar NNPP wanda ta shigo gari cikin ‘yan kwanakin nan tana cigaba da kara karfi a Najeriya, musamman Arewacin kasar inda har ta kai yanzu za su yi takarar Majalisar Dattawa a Jihar Bauchi.

An kara samun wanda zai yi takarar kujeran Sanatan Bauchi da ya rasu

Wani ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi ta kudu

Dr. Aliyu U. Tilde wani babban Marubuci kuma Masani a kan harkar Najeriya ya fito takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu. Kwanakin baya ne Sanata Aliyu Wakili wanda ke wakiltar yankin a Majalisar Dattawa ya rasu.

KU KARANTA: Ana rububin kujerar Bauchi ta Kudu a Najeriya

Aliyu Tilde ya bayyana cewa zai yi takarar ne a Jam’iyyar NNPP sai dai kuma zai iya gamuwa da cikas ganin cewa bai dade da shiga Jam’iyyar adawar ba. Tilde yana neman Jam’iyyar tayi masa lamuni ya fito takarar kujerar.

Babban Marubucin ya kuma bayyana cewa ba ya sha’awar tsayawa takara a Jam’iyyar PDP ganin yadda sunan Jam’iyyar ya baci a idanun jama’a ya kuma ce masu neman kujerar a Jam’iyyar APC sun yi yawa don haka ya shiga NNPP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel