Hargitsin majalisa a yau: Ekweremadu na ganawa da Osinbajo a Aso Rock

Hargitsin majalisa a yau: Ekweremadu na ganawa da Osinbajo a Aso Rock

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, a yanzu yana ganawa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Suna wannan ganawar sirri ne a ofishin mataimakin shugaban kasa a fadar Aso Rock.

Ana wannan ganawar ne bayan wasu yan baranda tare da Sanata Omo Agege suka kai farmaki majalisan inda suka sace sandar majalisan.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa da safen nan sanatan ya shigo harabar majalisan inda suka dauke sandar doka. Kakakin majalisar dattawa, Aliyu Sabi Abdullahi, ya tabbatar da hakan inda yace:

"A yau, wasu yan baranda karkashin jagorancin sanatan da aka dakatar, Ovie Omo-Agege, sun dira cikin majalisar dattawa suka sace sandar ikon majalisa".

KU KARANTA: Yan zanga-zanga sun kai farmaki majalisan dattawa, sun dauke sandar majalisa

"Wannan abu yakar kasa ne. Kuma wani yunkuri ne na juyin mulki ga wani reshen gwamnatin tarayya Najeriya. Dukkan hukumomin tsaro su tura jami'ansu domin tabbatar da cewa an dawo da sandar"

Daga baya, jami'an yan sanda sun damke Sanatan da ya turo yan ta'adda kuma an garkameshi

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel