Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron majalisan kasuwancin Commonwealth a Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron majalisan kasuwancin Commonwealth a Landan

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya samu daman halartan taron majalisan kasuwancin Commonwealth a yau Laraba, 18 ga watan Afrilu, 2018 a dakin taron Guild Hall, birnin Landan a kasan Birtaniya.

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a taron tare da shugaban CIMB Group Malaysia, Dato Seri Nazir Razak, Farfesa Ngaire Woods na jami’ar Oxford da kuma shugaban La Rue UK, Martin Sutherland.

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron majalisan kasuwancin Commonwealth a Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron majalisan kasuwancin Commonwealth a Landan

Wadanda suka takawa shugaba Buhari baya sune ministan kasuwanci da hannun jari, Okechukwu Enelamah, jakadan Najeriya zuwa Ingila, Amb. George Oguntade, mu’assasin Sahara Group Mr Tonye da shugaban bankin Chartered, Mrs Bola Adesola.

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron majalisan kasuwancin Commonwealth a Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron majalisan kasuwancin Commonwealth a Landan

KU KARANTA: Ma'aikatan jihar Katsina sun shiga tasku har shida sun mutu sakamakon rashin biyan albashin watanni 26

A jawabinsa, shugaba Buhari ya bayyana cewa yawancin matasan Najeriya da basu je makaranta ban a alfahari da cewa kasarsu na da arzikin man fetur saboda haka ba za su yi aiki ba kawai so suke su samu komai a banza.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel