Wani Mahaifi ya ƙone 'Dan sa da Dutsen guga mai zafi kuma ya antaya ma sa Fitsari

Wani Mahaifi ya ƙone 'Dan sa da Dutsen guga mai zafi kuma ya antaya ma sa Fitsari

Wani ma'aikacin jiragen ruwa, Blessing Erewa, ya kaiwa dan sa hari da dutsen guga mai zafin gaske, inda raunin da gadar masa a gadon baya ya yi sanadiyar gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo a ranar Larabar da ta gabata.

Erewa wanda mazanin unguwar Ifedolapo ta jihar Legas, ya harar wa dan nasa ne a bisa dalilin dawowa da yake gidan bayan dare ya raba.

Wani Mahaifi ya ƙone 'Dan sa da Dutsen guga mai zafi kuma ya antaya masa Fitsari

Wani Mahaifi ya ƙone 'Dan sa da Dutsen guga mai zafi kuma ya antaya masa Fitsari
Source: Twitter

Bayan yaron nasa mai sunan Marvelous ya dawo gida cikin dare kamar yadda ya saba, sai mahaifin sa Erewa ya hana shiga har zuwa wayewar gari.

KARANTA KUMA: An yiwa 'yar shekara 3 fyade har Lahira a jihar Kano

Wayewar gari ke da wuya Erewa cikin fushi ya daure Marvelous kuma ya dauko dutsen guga mai zafi ya dadara masa a gadon baya, sannan daga bisani kuma ya antaya masa fitsari a jiki.

A halin yanzu dai Erewa yana hannun hukuma duk da dai ya musanta zargin da ake a kan sa, inda alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Afrilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel