Zaben 2019: Zamu fito da dan takarar da yafi Buhari cancanta- PDP

Zaben 2019: Zamu fito da dan takarar da yafi Buhari cancanta- PDP

- Jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana sirrin yadda zasu kwace mulki a hannun APC cikin sauki

- Bayar da tikitin takara na kaitsaye ga Mutum daya na daga cikin matsalar da tayi sanadiyyar faduwar PDP zabe a 2015

A cigaba da karatowar zaben 2019, jam’iyyar PDP ta shirya tsaf domin kwace kujera daga hannun jam’iyyar APC ta hanyar fito da dan takarar da ya zarce Buhari nagarta

Hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar ta PDP, tsohon Ministan sufuri Chief Ebenezer Babatope, a yau Laraba yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

Zaben 2019: Zamu fito da dan takarar da yafi Buhari cancanta- PDP

Ebenezer Babatope

Yace, "A zabe mai zuwa, PDP zata nutsu tayi tunani sannan ta fitar da dan takarar da zai iya kawo wa Najeriya cigaban da yafi na gwamnatin shugaba Buhari. Wannan tabbaci ne ga yan Najeriya”.

Babatope ya kara da, jam’iyyar tasu ba za tayi la’akari da cewa ko babban dan siyasa ne ko karami ba, cancanta zasu bi su fitar da wanda zai yiwa talakawa aiki. Kuma zasu bayar da dama ga kowa ba tare da fifiko ba.

KU KARANTA: Malamai 12,000 sun soma aiki a makarantun jihar Kaduna, bayan an kori 'dakikan malamai

A cewarsa, PDP bata girgiza da jin sakewa tsayawar shugaba Buhari ba, domin yana da yan cin yin hakan.

Kuma ita ma PDP zata tabbatar ta tsaida wanda zai kayar da shugaba Buharin a zabe mai zuwa.

Babatope ya kuma bayyana jin dadinsa game da sulhun cikin gida da akai na jam’iyyar a shiyyar kudu maso yamma, sannan yace, “A yanzu muna cikin sha’anin sasantawa da rarraba mukamai ne kawai a shiyyar, kowa za’a tafi da shi ba tare da nuna fifiko ba”.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku

ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel