Yawanci matasan Najeriya basu son karatu, sun fi kaunar zaman kashe wando – Buhari daga Landan

Yawanci matasan Najeriya basu son karatu, sun fi kaunar zaman kashe wando – Buhari daga Landan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar mafi yawancin matasan Najeriya basu son yin karatu, sun fi kaunar zaman kashe wando ba tare da yin wani aiki fari ba balle na baki, inji rahoton The Cables.

Buhari ya bayyana haka ne a yayin taron kasashe rainon kasar Ingila, daya guda a Westminister dake birnin Landan a ranar Laraba, 18 ga watan Afrilu, inda yace yawancin matasan Najeriya basa zuwa Makaranta.

KU KARANTA: Mataimakin shugaban kasa ya maye gurbin Buhari a taron majalisar ministocin Najeiya

“Game da tattalin arzikin kasa, muna da miliyoyin matasa, don karamin hasashe ya nuna adadin yan Najeriya ya kai miliyan 180, a inda sama da kasha 60 na adadin yan kasa da shekara 30 ne, kuma da damansu basu zuwa makaranta, suna ganin ai Najeriya na da arzikin kasa, don sai dai ayi musu komai a kyauta.” Inji Buhari.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya yaba ma kansa game da abubuwa guda uku da ya kudiri magancewa a mulkinsa, inda yace:

“Munyi kokari matuka game da shawon kan matsalar tsaro, mun samu gagarumar nasara game da tattalin arzikin kasa, musamman a sha’anin noma, muna baiwa manoma bashi mai saukin ruwa, ta hanyar basu kayan aiki, magunguna da sauransu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel