Malamai 12,000 sun soma aiki a makarantun jihar Kaduna, bayan an kori 'dakikan malamai'

Malamai 12,000 sun soma aiki a makarantun jihar Kaduna, bayan an kori 'dakikan malamai'

- Gwamna ElRufai ya kori malamai ya kuma kwashi wasu

- Ya zargi wadancan da zama bara-gurbi da kuma dakikai da basu cancanci aikin ba

- Sabbin malaman sun kama aiki

Malamai 12,000 sun soma aiki a makarantun jihar Kaduna, bayan an kori 'dakikan malamai'

Malamai 12,000 sun soma aiki a makarantun jihar Kaduna, bayan an kori 'dakikan malamai'

Bayan da ya kori malaman makarantun Firamare a fadin jiharsa, wadanda suka kasa cin jarrabawar da marigayi tsohon kwamishina na ilimi, Mr. Andrew Nok ya shirya, gwamnan anzu ya sake daukar malamai da zasu koyar a fadin jihar.

Akalla sabbin malaman 11,395 ne aka dauka a sabon zubin, a wannan taragon, kuma gwamnatin ta fara waigar makarantun Sakandare, domin suma a tsarkake su.

DUBA WANNAN: An saki wani bidiyo kan Buhari da ba lallai yayi wa gwamnatin dadi ba

Koda yake a siyasance ace, kamar gwamnan ya caka wa kansa wuka ne, saboda korar malaman, gwamnan yace, hakan shine daidai, ko da kuwa zai kasa yin tazarce.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel