Tsautsayi: 'Daliban Najeriya 3 sun riga mu gidan gaskiya a kasar Kamaru

Tsautsayi: 'Daliban Najeriya 3 sun riga mu gidan gaskiya a kasar Kamaru

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Premium Times sun bayyana cewa, wasu Ɗalibai uku na jami'ar jihar Taraba sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyar tsautsayin ruwan sama na damuna inda wasu bishiyu suka fado ma su a filin shakatawa da bude ido na Bouba Njidda National Wild Life Park dake kasar Kamaru.

Kakakin wannan jami'a Sanusi Sa'ad, shine ya bayyana hakan a ranar Laraba ta yau yayin ganawa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na kasa a birnin Jalingo na jihar Taraba..

Mista Sa'ad ya bayyana cewa, wannan tsautsayi ya afku ne a yayin wani ruwan sama mai karfin gaske da misalin karfe 3.15 na yammacin ranar 16 ga watan Afrilu.

Ya ke cewa, Ɗaliban sun kasance a shekarar su ta karshe a fannin nazarin halittu inda ajali ya katse ma su hanzari a yayin da suke yawon karo ilimi a makociyar kasa ta Kamaru kasancewar ta tana iyaka ne da jihar Taraba.

KARANTA KUMA: Da dumi: Uwargidan tsohon Shugaban kasar Amurka ta riga mu gidan gaskiya

Kakakin ya bayyana sunayen Ɗaliban da suka riga mu gidan gaskiya kamar haka; Nancy Sam-Achak, Grace Thomas da kuma Yusuf Muhammad wanda ya kasance shugaban kungiyar dalibai dake fannin nazarin halittu watau Biology.

Ya kara da cewa, shugaban sashen nazarin halittu na jami'ar, Robert Houmso, yana daya daga cikinwanda suka raunata tare da dalibai a wannan tsautsayi, wanda a halin yanzu su na samun kulawa a asibitin Garoua na kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel