Majalisar Dattijai tayi wurgi da kudirin gyaran jadawalin zaben 2019

Majalisar Dattijai tayi wurgi da kudirin gyaran jadawalin zaben 2019

Majalisar dattawa tayi watsi da kudirin yin garambawul ga dokar zabe na 2010 wanda ke kokarin canja jadawalin zaben 2019 da ke kokarin mayar da zaben shugaban kasa ya zamo na karshe.

Kudirin da ke ake sa ran gabatar dashi saboda karantawa na biyu ya samu tangarda ne bayan sanatoci da dama sun tafka muhawara a kansa da irin abubuwan da canja jadaalin zaben zai haifar.

Yan majlisaar sun yanke shawarar watsi da kudirin kuma sun umurci kwamitin majalisar na zabe ya cire canje-canjen da kayi niyyar yi wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari yaki amincewa da ita.

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta hakura da batun canja jadawalin zabe

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta hakura da batun canja jadawalin zabe

DUBA WANNAN: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da Sanata Ovie Omo-Agege

Daga baya za'a mayar wa fadar shugaban kasa kudrin indan an cire sashin da yaki amincewa dashi din don ya sanya hannu.

Idan ba'a manta ba wannan kudirin ne yayi dalili majalisar da dakatar da Sanata Ovi Omo-Agege a yayinda ya goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel