Da dumi-dumi: Jami’an yan sanda sun damke Sanatan da ya sace sandar majalisa

Da dumi-dumi: Jami’an yan sanda sun damke Sanatan da ya sace sandar majalisa

Jami’an yan sanda sun damke sanatan da ya jagoranci yan daba suka hargitsa majalisa suka sace sandaar majalisa a yau Laraba, 18 ga watan Afrilu, 2018.

Kwamishanan yan sandan birnin tarayya Abuja, Sadiq Abubakar Bello, da kansa ne ya jagoranci tawagar da suka tafi da shi.

Mun kawo muku cewan Sanatan da aka dakatar, Ovie Omo-Agege, ya dawo majalisan dattawan a yanzu kuma yana zaune cikin abokan aikinsa ana zaman majalisa.

Da dumi-dumi: Jami’an yan sanda sun damke Sanatan da ya sace sandar majalisa

Da dumi-dumi: Jami’an yan sanda sun damke Sanatan da ya sace sandar majalisa

Yayin dawowanshi ne jami'an yan sanda suka samu daman damke shi.

Legit.ng Zangon majalisar dokoki ta umurci Sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris da ya tabbatar da an dawo da sandar iko na majalisa cikin sa’o’i ashiri da hudu.

KU KARANTA: Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege ya dawo majalisa

Hakan ya biyo bayan yan daban da ake kyautata zaton cewa yan zanga-zanga magoya bayan sanatan da aka dakatar ne, Senata Ovie Omo-Agege sun kai hari majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel