Yanzu-yanzu: Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege ya dawo majalisa

Yanzu-yanzu: Sanatan da aka dakatar, Omo-Agege ya dawo majalisa

Sanatan da aka dakatar, Ovie Omo-Agege, ya dawo majalisan dattawan a yanzu kuma yana zaune cikin abokan aikinsa ana zaman majalisa.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa da safen nan sanatan ya shigo harabar majalisan inda suka dauke sandar doka. Kakakin majalisar dattawa, Aliyu Sabi Abdullahi, ya tabbatar da hakan inda yace:

"A yau, wasu yan baranda karkashin jagorancin sanatan da aka dakatar, Ovie Omo-Agege, sun dira cikin majalisar dattawa suka sace sandar ikon majalisa".

KU KARANTA: Yan zanga-zanga sun kai farmaki majalisan dattawa, sun dauke sandar majalisa

"Wannan abu yakar kasa ne. Kuma wani yunkuri ne na juyin mulki ga wani reshen gwamnatin tarayya Najeriya. Dukkan hukumomin tsaro su tura jami'ansu domin tabbatar da cewa an dawo da sandar"

"Majalisa na ganawar gaggawa yanzu kuma zamu kawo muku cikakken rahoton anjima" .

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel