Dalilin da yasa Najeriya ke cikin damuwa - Tinubu

Dalilin da yasa Najeriya ke cikin damuwa - Tinubu

- Shugaban jam’iyyar APC na kasa Bola Tinubu, ya sake jingina laifi ga gwamnatin data gabata ta Jonathan akan matsalar tattalin arzikin kasa

- Tinubu wanda Abiol Ajimobi ya wakilta yace, gwamnatin Jonathan itace wadda tafi kowace koma baya a cikin gwamnatocin da akayi a Najeriya

- Tinubu yace matsalar tsayawar ayyukan cigaba da ake ta fuskanta ya faru ne sakamakon biliyoyin kudade da aka sata lokacin gwamnatin data gabata

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Bola Tinubu, ya sake jingina laifi ga gwamnatin data gabata ta Jonathan akan matsalar tattalin arzikin kasa da aketa korafi akai.

Tinubu wanda gwamna Abiol Ajimobi ya wakilta a wurin taron da aka gudanar a jihar Kano na tinawa da Malam Aminu Kano yace, gwamnatin Jonathan itace wadda tafi kowace koma baya a cikin gwamnatocin da akayi a Najeriya.

Dalilin da yasa Najeriya ke cikin damuwa - Tinubu

Dalilin da yasa Najeriya ke cikin damuwa - Tinubu

A cikin wadanda sukayi jawabi a wurin taron sun hada Dapo Olorunyomi, mai watsa labarai na Premium Times, sai kuma daya daga cikin jajirtattun ‘yan jam’iyyar APC, Dr. Usman Bugaje.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta bukaci a dawo da sadar iko cikin sa’o’i 24 bayan yan daba sun arce da ita

Tinubu yace matsalar tsayawar ayyukan cigaba da ake ta fuskanta ya faru ne sakamakon biliyoyin kudade da aka sata lokacin gwamnatin data gabata, wanda da za’ayi amfani dasu a kasar nan ayi aiki da an sauya kasar baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel