Za mu iya rufe Majalisa domin tallafawa Buhari kawo karshen kashe-kashe - Ekweremadu

Za mu iya rufe Majalisa domin tallafawa Buhari kawo karshen kashe-kashe - Ekweremadu

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ya bayyana cewa ta yiwu a rufe majalisa domin tallafawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari gano bakin zare da zai kawo karshen kashe-kashe da makiyaya ke ta faman aikatawa a fadin kasar nan.

Majalisar ta kuma yi gargadi akan abinda zai iya dakile zuba hannayen jari na kasashen waje a kasar nan muddin rashin tsaro ya ci gaba da ta'azzara a cikin ta.

Ekweremadu wanda ya jagoranci zaman majalisa na ranar Talatar da ta gabata ya bayyana hakan ne a yayin tsawatar da Sanata Suleiman Adokwe mai wakilcin Kudancin jihar Nasarawa da ya yi korafin kashe-kashen dake faman afkuwa a mazabar sa.

Za mu iya rufe Majalisa domin tallafawa Buhari kawo karshen kashe-kashe - Ekweremadu

Za mu iya rufe Majalisa domin tallafawa Buhari kawo karshen kashe-kashe - Ekweremadu

Adokwe wanda ya bayyana cewa kawowa yanzu hankalin al'ummar mazabar sa a tashe yake sakamakon adadin rayukan da suka salwanta, jikkatar da dama gami da daruruwan mutane da suka yi gudun hijira.

Sanatan ya yi la'akari da tsohon shugaban hafsin sojin kasa kuma tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Danjuma, da ya kirayi al'ummar Najeriya akan su tashi tsaye domin kare kawunan su, idan yace tabbas wannan kira na shi a halin yanzu ya dace da daidai.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta tabbatar da amincin mukaman shugaban NHRC da shugaban NERC

A sanadiyar haka ne mataimakin shugaban majalisar yake cewa, a halin yanzu akwai bukatar majalisar dokoki ta kasa ta taka rawar gani domin ganin karshen kashe-kashe da zubar da jini a fadin kasar nan.

Yake cewa, ba bu yaddaza a yi majalisa za ta ci gaba da kasancewa matukar ba bu mutanen da za ta yiwa wakilci, kuma ba bu yadda za a yi zabe ya tabbata muddin masu kada kuri'u ba sa raye.

Ekweremadu ya kara da cewa, muddin lamarin ya kai wani mataki ba bu makawa face rufe majalisa domin zama tare da gwamnati wajen gano hanyar magance matsalar ta dindindin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel