Kungiyoyi masu goyon bayan Atiku sunyi barazanar juya masa baya

Kungiyoyi masu goyon bayan Atiku sunyi barazanar juya masa baya

- Kungiyoyi masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban shugaban, Atiku Abubakar sunyi barazanar janye goyon bayan su gareshi a zaben 2019

- Kungiyoyin sunyi wannan barzanar ne saboda kudaden rajista da sukayi ikirari ana karba daga hannunsu a ofishin kamfen din Atiku da ke Abuja

- Sai dai Direktan Kungiyar matasa magoya bayan Atiku, Nath Yaduna, yace bashi da hannu cikin wannan badakalar

Bisa ga dukkan alamu za'a iya samun tangarda wajen yakin neman zaben shugabancin kasa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, keyi gabanin zaben 2019 saboda zargin karbar kudade da akeyi daga kungiyoyi masu goyon bayan Atikun a ofishin Kamfen dinsa na Abuja.

Kungiyoyi masu goyon bayan Atiku sunyi barazanar juya masa baya

Kungiyoyi masu goyon bayan Atiku sunyi barazanar juya masa baya

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa bincike da aka gudanar a Abuja ya bayyana cewa wani daga cikin ma'aikaci ofishin yakin neman zaben Atiku wanda ba'a bayyana sunansa ba wai ya gayyaci kungiyoyi 46 masu goyon bayan Atiku a ranar Lahadi 15 ga watan Afrilu inda ya bukaci su biya wasu kudaden rajista idan suna son kungiyar kamfen din Atiku ta amince da su.

DUBA WANNAN: Soji na neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

Legit.ng ta tattaro cewa wata majiya da ke wajen taron tace an bukaci kowanne kungiya ta biya N10,000 kafin Ofishin kamfen din na Atiku da amince da su.

A yayin da suke mayar da martani akan badakalar kudin, Kungiyoyin magoya bayan Atikun sunyi gargadin cewa idan har ba'a gudanar da bincike an dauki mataki kan ma'aikacin da ke aikata wannnan abin ba za su janyo goyon bayan nasu ga Atiku.

A jawabin da yayi kan batun, Sakatare na kasa na kungiyar matasa magoya bayan Atiku, Kwamared Samuel Tiku yace za'a gudanar da bincike saboda idan ba'a dauki mataki ba hakan zai iya haifar da matsala ga yakin neman zaben na Atiku.

Kazalika, Direktan Atiku Youth Organisation, Nath Yaduna, yace bashi da masaniya akan lamarin kuma ya kara da cewa kungiyar basu bayar da umurnin a karba kudin rajista daga kungiyoyin magoya bayan Atiku ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel