Rikicin ‘Yan Shi’a: Kungiyar Amnesty ta fadawa gwamnatin tarayya cewa kada ta tauyewa yan Najeriya hakkinsu

Rikicin ‘Yan Shi’a: Kungiyar Amnesty ta fadawa gwamnatin tarayya cewa kada ta tauyewa yan Najeriya hakkinsu

- Kungiyar bayar da kariya ta duniya ta fadawa gwamnatin tarayya cewa kada ta hanawa mutanen kasar ta hakkinsu, wadanda ke gabatar da zanga-zangar lumana

- Daraktan kungiyar bayar da kariya ta duniya, wadda ke Najeriya Miss Osai Ojigho, lokacin da take nuna rashin kyautawa akan hana kungiyar ‘yan Shi’a zanga-zanga a birnin tarayya

- ‘Yan kungiyar ta Shi’a suna tafiya ne a hanyar Berger Junction lokacin da jami’an ‘Yan Sanda suka fara watsa masu ruwan zafi da barkonon tsohuwa

Kungiyar bayar da kariya ta duniya ta fadawa gwamnatin tarayya cewa kada ta hanawa mutanen kasar ta hakkinsu, wadanda ke gabatar da zanga-zangar lumana ta bukatar zakin shugabansu da matarsa.

Daraktan kungiyar bayar da kariya ta duniya, wadda ke Najeriya Miss Osai Ojigho, lokacin da take nuna rashin kyautawa akan hana kungiyar ‘yan Shi’a zanga-zanga a birnin tarayya, a jawabin da tayi a ranar Talata.

Rikicin ‘Yan Shi’a: Kungiyar Amnesty ta fadawa gwamnatin tarayya cewa kada ta tauyewa yan Najeriya hakkinsu

Rikicin ‘Yan Shi’a: Kungiyar Amnesty ta fadawa gwamnatin tarayya cewa kada ta tauyewa yan Najeriya hakkinsu

‘Yan kungiyar ta Shi’a suna tafiya ne a hanyar Berger Junction lokacin da jami’an ‘Yan Sanda suka fara watsa masu ruwan zafi da barkonon tsohuwa, wanda hakan yasa dole suka bar zanga-zangar, wadda sukeyi don a saki shugabansu Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat.

KU KARANTA KUMA: 30 ne kadai cikin ‘yan makarantar Chibok ke raye - Ahmad Salkida

Ojigho tace ‘Yan Shi’an sunyi taron zanga-zangar kan ka’ida a birnin tarayyar don neman a saki shugaban nasu daga hannun gwamnati, duk da cewa akwai rahotannin cewa sun jefi jami’an tsaron, amma dai hakan bai bayar da damar a watsa masu ruwan zafi ba da barkonon tsohuwa ba.

Tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta El-Zakzaky da matarsa, sannan ta bincika kisan da akayi a watan Disamba 12 zuwa 14 shekarar 2015, a garin Zaria. Saboda kama wasu mutane 115 cikin ‘yan Shi’ar yana nuna Karin damuwa na cewa zanga-zangar zata cigaba

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel