Ka ceto 'yan Matan Chibok da Leah kafin zaben 2019 - Majalisar Wakilai ga Shugaba Buhari

Ka ceto 'yan Matan Chibok da Leah kafin zaben 2019 - Majalisar Wakilai ga Shugaba Buhari

A ranar Talatar da gabata ne majalisar wakilai ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya gaggauta ceto ragowar 'yan matan Chibok 113 da kuma dalibar Dapchi ta karshe, Leah Sharibu dake hannun 'yan ta'adda kafin zaben 2019.

Majalisar ta kuma bayyana damuwar ta dangane da ikirarin gwamnatin tarayya na sayen kayan yaki ga dakarun soji daga kasar Amurka na kimanin $460m ba tare da amincewar majalisar dokokin tarayya ba.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, wannan kudade daban su ke da $1bn na kwana-kwanan nan da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da amincewar sayowa dakarun soji kayan aiki.

Ka ceto 'yan Matan Chibok da Leah kafin zaben 2019 - Majalisar Wakilai ga Shugaba Buhari

Ka ceto 'yan Matan Chibok da Leah kafin zaben 2019 - Majalisar Wakilai ga Shugaba Buhari

Mambobin majalisar sun nuna damuwar su kwarai da aniyya a yayin tafka muhawara kan makomar 'yan Matan Chibok, inda suke cewa wannan abin kunya ya kai makura ta kusan shekaru hudu da gwamnati ta gaza ceto su daga hannun 'yan ta'adda na Boko Haram.

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya kar abokin sa sakamakon kin amincewa da kwazabar sa ta neman Maza

Majalisar ta lura da cewa, duk da kasancewar gwamnati tayi nasara sanasanta sako mafi akasarin 'yan matan dapchi, wannan kokari ba zai yi tasairi a ma'aunin nasara ba muddin Leah Sharibu ta ci gaba da kasnacewa a hannu masu garkuwa da ita.

Legit.ng ta fahimci cewa, 'yan majalisa mai wakilcin mazabar Damboa da Chibok ta jihar Borno, Misis Asabe Bashir, ita ta fara kawo wannan batu a majalisar yayi da Kakakin ta Mista Yakubu Dogara ya jagoranci zaman da aka gudanar.

Dogari ya janyo hankalin gwamnatin tarayya akan ta tashi tsaye wajen ceto 'yan matan kafin zabe na 2019 ya wakana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel