An yiwa yarinya ‘yar shekara 3 fyade har ta mutu, a jihar Kano

An yiwa yarinya ‘yar shekara 3 fyade har ta mutu, a jihar Kano

- An samu gawar Khadijah Abubakar Abdullahi ‘yar shekara 3 da haihuwa wadda ta bata tun kwanaki hudu da suka gabata a cikin wani Ofishi

- Binciken jami’an ‘Yan Sanda ya nuna cewa anga alamun jini a gaban yarinyar, wanda hakan ya nuna cewa anyiwa Khadijah fyade ne

- Kano Chronicles sun bayyana cewa Khadijah ta bata ne bayan sun tafi makaranta tare da ‘yan uwanta su biyu

An samu gawar Khadijah Abubakar Abdullahi ‘yar shekara 3 da haihuwa wadda ta bata tun kwanaki hudu da suka gabata a cikin wani Ofishi na makarantar kauyen Khairat, a Walalambe quarters, karamar hukumar Nasarawa.

Binciken jami’an ‘Yan Sanda ya nuna cewa anga alamun jini a gaban yarinyar, wanda hakan ya nuna cewa anyiwa Khadijah fyade ne, kuma ba’a kaiga sanin ko wanene ya aikata wannan mummunan aiki ba.

An yiwa yarinya ‘yar shekara 3 fyade har ta mutu, a jihar Kano

An yiwa yarinya ‘yar shekara 3 fyade har ta mutu, a jihar Kano

Kano Chronicles sun bayyana cewa Khadijah ta bata ne bayan sun tafi makaranta tare da ‘yan uwanta su biyu, inda maman tata ke koyarwa.

KU KARANTA KUMA: 30 ne kadai cikin ‘yan makarantar Chibok ke raye - Ahmad Salkida

SP Magaji Musa Majia, jami’in ‘Yan Sanda mai kula da harkokin jama’a, ya tabbatar mana da cewa an kama malami tara daga cikin malaman makarantar wadanda ake zargin cikinsu ne wani ya aikata hakan, sannan ya tabbatar da cewa cikin kwanaki hudu zasu gano wanda ya aikata wannan mummunan aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel