30 ne kadai cikin ‘yan makarantar Chibok ke raye - Ahmad Salkida

30 ne kadai cikin ‘yan makarantar Chibok ke raye - Ahmad Salkida

- Dan Jaridar da shi kadai ne keda hanyar samun labarai daga kungiyar ‘yan Boko Haram Ahmad Salkida ya bayyana cewa 30 kadai cikin ‘yan matan Chibok ke raye

- Hakan ya sabawa labarain da ‘yan jarida suka ruwaito a baya cewa 15 ne cikin ‘yan matan Chibok suke da rai a cikin wadanda suka rage a hannun kungiyar

- Salkida a bayyana haka ne a kafar sadarwa ta Tuwita bayan watanni da dama da ba’a magana a kan ‘yan matan na Chibok

Dan Jaridar da shi kadai ne keda hanyar samun labarai daga kungiyar ‘yan Boko Haram Ahmad Salkida ya bayyana cewa 30 kadai cikin ‘yan matan Chibok ke raye.

Hakan ya sabawa labaran da ‘yan jarida suka ruwaito a baya cewa 15 ne cikin ‘yan matan Chibok suke da rai a cikin wadanda suka rage a hannun kungiyar ta Boko Haram.

30 ne kadai cikin ‘yan makarantar Chibok ke raye - Ahmad Salkida

30 ne kadai cikin ‘yan makarantar Chibok ke raye - Ahmad Salkida

Salkida a bayyana haka ne a kafar sadarwa ta Tuwita bayan watanni da dama da ba’a magana a kan ‘yan matan na Chibok, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan matan sunyi aure kuma ’yan Boko Haram dinne suka aura, wasu ma har an kashe mazajen nasu a arangamar da sukeyi da Sojojin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Ni ba Bahaushiya bace sannan ina jin dadin rayuwar aurena - Fatima Ganduje

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Boko Haram (Jama’atul Ahlis-Sunna Lidda’awati Wal-Jihad) ya tabbatar mani a yau cewa 15 daga cikin ‘yan matan na Chibok ke raye, kuma suna cikin wani dakin kurkuku daban, ya bayyana mani hakane gabanin bikin watsa labarina na 4.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel