An yiwa 'yar shekara 3 fyade har Lahira a jihar Kano

An yiwa 'yar shekara 3 fyade har Lahira a jihar Kano

An tsinto gawar wata yarinya Khadija Abubakar Abdullahi 'yar shekaru 3 bayan an neme ta an rasa kwanaki hudu da suka gabata a cikin wani ofishin makarantar Khairat Community School dake unguwar Walalambe a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

Jaridar Kano Chronicle ta ruwaito cewa, binciken hukumar 'yan sanda ya bayyana yadda aka tsinto gawar dauke cikin jini da ya fito daga gaban yarinyar wanda ya tabbatar da cewa an yi lalata da ita.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, an nemi Khadija an rasa bayan ita da 'yan uwanta biyu suka tafi makarantar ta Khairat inda mahaifiyar su tana daya daga cikin Malamai a makarantar.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar SP Magaji Musa Majia, ya tabbatar da afkuwar wannan abin takaici inda ya ce a halin yanzu mutane 9 da ake zargi sun shiga hannu wanda mafi akasarin su malaman makarantar ne.

An yiwa 'yar shekara 3 fyade har Lahira a jihar Kano

An yiwa 'yar shekara 3 fyade har Lahira a jihar Kano

A yayin shigar da rahoto ga jami'an 'yan sanda, mahaifin wannan yarinya, Mallam Abubakar Abdullahi wanda ya shahara da sunan IBB, ya bayyana cewa yayi kacibus ne da gawar 'yar sa a tsirara kwance cikin jini wanda ya fito daga gaban ta da kuma baya.

KARANTA KUMA: Cututtuka 9 da Ganyen Gwanda ke kawarwa a jikin dan Adam

Mallam Abubakar ya bayyana cewa, ya tsinci gawar marigayiya Khadija ne a yayin da ta fara rubanyewa tare da samami da yake tashi, wanda wannan yanayi da ya ga diyar sa ya sanya ya kasa kai hannu a gareta, ya kuma garzaya cikin gaggawa zuwa ga hukumar 'yan sanda domin su binciki lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa, an yi ta cigiyar Khadija a gidajen makwabta da 'yan uwa tun bayan da 'yan uwanta suka dawo daga makaranta kuma suka labarta cewa sun neme ta sun rasa, wanda a wannan lokaci an yi rashin sa'a mahaifiyar ba ta je aiki sakamakon hali na rashin lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel