An yi tir da Festus Keyamo na karbar aikin yakin neman zaben Buhari a 2019

An yi tir da Festus Keyamo na karbar aikin yakin neman zaben Buhari a 2019

Mun fahimci cewa Babban Lauyan Najeriya Festus Keyamo SAN yana cigaba da shan suka daga jama’a da dama bayan an nada shi a matsayin mai magana da bakin kwamitin da ke fafatukar yakin neman zaben Shugaba Buhari a 2019.

Kwanan ne Festus Keyamo wanda Lauya ne da ke kare hakkin Bil Adama a Najeriya ya bayyana cewa an nada shi a matsayin kakakin tazarcen Shugaba Buhari a 2019. Wasu na ganin Keyamo ya bada maza da ya amsa wannan goro saboda zargin da ke wuyan Gwamnatin nan.

An yi tir da Festus Keyamo na karbar aikin yakin neman zaben Buhari a 2019

Jama'a su na cigaba da Festus Keyamo na zama kakakin neman tazarcen Buhari

Tun kafin a je ko ina wani rikakken Farfesan Turanci Farouk Kperogi yace yanzu Lauyan lomar tuwon sa kurum yake karewa. Shi ma wani Bawan Allah mai suna Kelvin Odanz yace abin da ban mamaki ace Keyamo na aiki da Gwamnatin da ta hallaka Yan Shi’a.

KU KARANTA: Ana neman Buhari ya bayyana abin da ya kashe a asibiti

Orji Uka ma dai ya koka a shafin sa na Tuwita inda yace a rasa inda Barista Keyamo zai yi aiki sai a Gwamnatin da ta saba keta alfaramar jama’a tana kuma sabawa dokar Kotu. Shigen dai abin da wani Bawan Allah mai suna JAGABAN ya fada kenan a jiya.

Ana zargin Gwamnatin nan da tsare Jagoran ‘Yan Shi’a Zakzaky babu gaira babu dalili duk da Kotu tace a sake sa. Haka kuma dai Sambo Dasuki yana hannun Hukuma har yanzu duk da umarnin Kotu. Wasu na ganin cewa bai dace Keyamo ya amsa wannan tayi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel