Soji na neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

Soji na neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

- Hukumar Sojin Najeriya ta bayar da sanarwan neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

- Hukumar Sojin tace ana neman su ne saboda ana zarginsu da hannu cikin kashe-kashen da akayi a wasu sassan jihar

- Sojin ta sharwarci al'umma su kasance masu taimakawa jami'an tsaro da bayanai masu amfani saboda daukan mataki cikin gagawa

A yunkurin ta Hukumar Sojin Najeriya keyi na magance tashe-tashen hankula da ke faruwa a wasu sassan jihar Taraba karkashin atisayen Ayem Akpatuma, sojin ta bayar da sanarwan neman wasu mutane 5 a jihar Taraba.

Kamar yadda sanarwan da kakakin hukumar sojin Najeriya, Brig. Janar Texas Chukwu ya aike wa Legit.ng, ana neman mutanen biyar ruwa a jallo ne saboda ana zargin su da hannu cikin kashe-kashen da akayi a karamar hukumar Takum da sauran sassan jihar Taraba.

Soji na neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

Soji na neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe mutum biyu a wajen wani biki

Sunayen wadanda ake neman sun hada da:

1) Mr. Tanko Adiku Dantayi

2) Mr Kurusi Danladi

3) Mr Chindo

4) Mr Big Olumba

5) Sai kuma wani da ake kira Chairman Poko

Sanarwan kuma tace, "Ana shawartan al'umma su cigaba da bawa jami'an tsaro bayanai masu amfani akan lokaci saboda daukan matakin gagagwa."

Soji na neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

Soji na neman wasu mutane 5 ruwa a jallo a jihar Taraba

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel