Likitar FMC ta kashe mana danmu – Iyaye

Likitar FMC ta kashe mana danmu – Iyaye

Ahlin Joseph Mbonu, iyayen wani yaro dan watanni tara, Jidenma Mbonu, wanda ya mutu ranar Juma’a da ta gabata a babban asibitin Yenagoa, jihar Bayelsa sun zargi wata likiyta mace da kashe masu dansu.

Sunyi zargin cewa sun rasa yaron nasu a asibitin bayan likitar ta yi masa allura da maganin day a haura misali.

Mahaifiyar yaron tayi zargin cewa a lokacin da likitar da ake Magana a kanta ta zo ta gauraya maganin sannan ta girgiza wajen kimanin mintuna 30.

Tayi ikirarin cewa “wata likita ta tambayeta dalilin da yasa take ta girgiza maganin na tsawon lokaci. Amma sai likitar tace tana yi ne domin ya hadu da kyau. Na tuna mata cewa ana raba maganin gida biyu sannan ayi amfani da 2ml. Amma sai na nemi sanin dalkilin da yasa tayi amfani da 5ml akan dana. Sai tace mun zan koya mata aikinta ne?

“Na fito da kafar dana: sai tayi amfani da alluran 5ml tayi masa alluran farko cikin sauri. Ta sake yin na biyu da uku. Daga nan sai yarona ya fara amai a jikina sannan ya fara rawar dari. Dana ya mutu a hannu na.”

KU KARANTA KUMA: Mutumin da ya rayu tsawon watanni ba fuska ya samu sauki

Mahaifin yaron ya roki yan sanda da sauran hukumomin da su kawo masu agaji.

Ya sha alwashin yin amfani da mutuwar dansa wajen yaki da rashin adalci da akewa yara a asibitoci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel