Zaben 2019: Matasa sun fara harin kujerar Shugaban kasa a Najeriya

Zaben 2019: Matasa sun fara harin kujerar Shugaban kasa a Najeriya

Matasa sun danno kai domin ganin sun karbe ragamar mulkin Kasar nan. Daga cikin masu shirin yin takarar Shugaba kasar a 2019 mun kawo wasu 3 da su kayi fice a halin yanzu. Sai dai har yanzu akwai alamar tambaya ko za su iya yin nasara.

Daga cikin masu harin kujerar Shugaba Buhari akwai mai gidan Jaridar Sahara Reporters watau Omoyele Sowore. Ga dai sunayen su nan:

Zaben 2019: Matasa sun fara harin kujerar Shugaban kasa a Najeriya

Omoyele Sowore ya sha alwashin zama Shugaban kasar Najeriya

1. Omoyele Sowore

Sowore mai shekaru 47 a Duniya ya bayyana cewa zai yi takara a 2019. A makon nan Sowore ya gana da Sheikh Ahmad Gumi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da kuma Balarabe Musa duk don ganin ya samu nasara.

KU KARANTA: Bola Tinubu ya bayyana matsalar da Shugaba Buhari ya ke fuskanta

2. Adamu Garba II

Adamu Garba wanda asalin mutumin Jihar Adamawa ne ya dage wajen ganin ya tika Shugaba Buhari da kasa a 2019 a Jam'iyyar sa ta APC. Yanzu haka dai Garba ya fara neman gudumuwar kudin takarana zaben mai zuwa.

3. Ahmed Buhari

Na uku a jerin shi ne Ahmad Buhari wanda 'Dan kasuwa ne a Legas mai shekaru 38 yana kuma ganin shi ya cancanci ya canji Shugaban kasa Buhari. Buhari dai Saurayi ne da ba ya nuna bambancin kabila ko Jihar mutum.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel