Halin da jihar Gombe ke ciki dangane da yawaitar fyade - Gwamna Dankwambo

Halin da jihar Gombe ke ciki dangane da yawaitar fyade - Gwamna Dankwambo

Matsalar fyade na cigaba da yaduwa a tsakanin al'umma da kabilun duniya. Najeriya ma na fama da wannan mugunyar matsala a sassan kasar daban-daban.

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya koka bisa yawaitar afkuwar fyade a jihar sa tare da yin kiran a hada karfi da karfe domin yakar wannan annoba.

"Matsalar fyade a jihar Gombe kullum karuwa take yi domin yanzu haka ta kai ga a kullum sai an yiwa a kalla yara biyu fyade a kullum. Wannnan shine matsayin da illar fyade ta kai a jihar Gombe," a cewar Dankwambo yayin da ya karbi bakuncin kungiyar mata lauyoyi, reshen jihar.

Halin da jihar Gombe ke ciki dangane da yawaitar fyade - Gwamna Dankwambo

Gwamna Dankwambo

Kungiyar mata lauyoyi sun kaiwa gwamnan ziyarar ban girma ne ranar Talata a bikin mako da kungiyar ke yi duk shekara.

Dankwambo ya kara da cewar, a daya daga cikin rahotannin fyade a jihar, an taba samun wani dattijon biri mai shekaru 60 na aikata fyade ga wata yarinya mai shekaru hudu.

DUBA WANNAN: An gano gawarwakin 'yan sanda 6 da aka kashe jiya a Benuwe

Gwamnan ya shaidawa kungiyar lauyoyi matan cewar gwamnati kadai ba zata iya magance wannan matsala ba tare da yin kira ga lauyoyin da su bawa gwamnati goyon baya da hadin kai domin yakar wannan musifa.

Daga karshe gwamnan ya yiwa kungiyar alkawarin cewar kwanan nan za a bude sashen ilimin shari'a a jami'ar gwamnatin jihar (GSU).

Da take jawabi, shugabar kungiyar lauyoyi Mata reshen jihar Gombe, Sa'adatu Ishaya, ta shaidawa gwamnan cewar kungiyar su zata zama gatan maras gata musamman ga mata da kananan yara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel