Mutumin da ya rayu tsawon watanni ba fuska ya samu sauki

Mutumin da ya rayu tsawon watanni ba fuska ya samu sauki

Rahoatanni sun kawo cewa mutumin da aka yiwa dashen fuska har sau biyu cikin watanni uku a duniya ya samu afuwa sosai.

A shekarar da ta gabata ne aka cire wa Jérôme Hamon fuskar farko inda aka dasa masa bayan da alamu suka nuna jikinsa ya ki karbar fuskar sakamakon shan wani maganin kashe kwayoyin cuta da ya yi na mura.

Mutumin mai shekara 43 a duniya ya kasance a wani asibiti a Paris ba tare da fuska a jikinsa ba har tsawon wata biyu, a lokacin ana neman wanda zai bayar da gudunmuwar fuska.

Ya ce da farko jikinsa ya karbi fuskar farko, yanzu ma haka, fuskar da aka sanya masa wa jikin nasa ya karbeta.

Mista Hamon na fama ne da wata larura mai haddasa kulayen da ke bata fuska wacce ake kira neurofibromatosis type 1.

Mutumin da ya rayu tsawon watanni ba fuska ya samu sauki

Mutumin da ya rayu tsawon watanni ba fuska ya samu sauki

Dashen da aka yi masa na farko a 2010 ya yi nasara, amma a 2015 ya kamu da mura inda aka bashi maganin kashe kwayoyin cuta (wato antibiotics).

Sai dai maganin bai dace da magungunan da ake ba shi ba, saboda haka kwayoyin halittar jikinsa su ka ki karbar dashen da aka yi masa.

A nan ne aka cire fuskar da aka dasa masan, ya kuma zauna tsawon wasu lokuta kafin a dasa masa wata inda ya kasance a asibiti ba ya ji ba ya gani.

Mista Hamon ya rayu babu fuska a wani daki a asibitin Georges-Pompidou na birnin Paris - inda a lokacin ba ya iya gani, ko magana ko jin sauti har sai da aka sami wanda ya bayar da fuskarsa ga mai bukata.

KU KARANTA KUMA: Tarihin rayuwa da siyasar 'Jagoran Talakawa' Aminu Kano

A lokacin ne aka dasa masa fuskar bayan da aka yi wani aikin tiyata, domin ka da jikin Mista Hamon ya ki karbar sabuwar fuskar da aka dasa masa, an gudanar da wani aiki na musamman domin tsaftace jinin jikinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel