Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kama dan leken asirin 'yan Boko Haram

Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kama dan leken asirin 'yan Boko Haram

Rundunar dakarun sojojin Najeriya a jiya ta bayar da labarin samun nasarar da suka yi na fatattakar wasu 'yan Boko Haram tare da kashe bakwai daga cikin mayakan su a wani gumurzu da akayi a cikin dazukan jihar Borno.

Kanal Onyema Nwachukwu dake zaman mataimakin daraktan dundunar tabbatar da zaman lafiya dake yaki da 'yan ta'addan ne dai ya sanar da hakan ga manema labarai a can garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kama dan leken asirin 'yan Boko Haram

Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kama dan leken asirin 'yan Boko Haram

KU KARANTA: Rikici na shirin kunno kai game da azumin bana a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa haka zalkika kamar dai yadda ya shaidawa majiyar mu, rundunar ta su ta kuma samu nasarar kama wani wanda ke yi wa 'yan ta'addan leken asiri mai suna Modu Chari.

A wani labarin kuma, Yan majalisar dattijan Najeriya sun zargi ministocin kudade da kuma na tsaro a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari gami da shugaban babban bankin Najeriya na CBN da hada baki wajen fitar da makudan kudaden da suka kai $462 miliyan don siyen jirgin yaki mai saukar angulu.

Yanzu haka dai tuni har majalisar dattijan ta aiki da takardar sammaci zuwa ga jami'an gwamnatin da suka ce suna so su bayyana a gaban su domin bayar da ba'asi kan yadda akayi har hakan ta faru.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel