Ku sadu da budurwa mai shekaru 25 wadda ta kammala digirin digir-gir daga Arewa
Wani abun alfahari ya samu al'ummar arewacin Najeriya bayan da aka samu wata budurwa mai matukar kananan shekarun da ba su zarce 25 ba a duniya da ta kammala digirin digir-gir a jami'ar Covenant mai suna Chiamaka Deborah Motilewa.
KU KARANTA: Zaftarewar kasa tayi sanadin ajalin mutum 3 a Arewa
A cikin yanayi mai cike da shauki ne dai budurwar ta sanar da hakan a shafin ta na dandalin sadar da zumunta na Tuwita inda ta bayyana cewa ta samu kammala karatun na ta ne a bangaren harkokin kasuwanci.
Legit.ng dai ta samu cewa Dakta Chiamaka Deborah Motilewa yar asalin jihar Kogi ce dake a Arewacin Najeriya ta tsakiya sannan kuma an haife ta kuma girma a garin Jos.
Daman dai ko shakka babu yankin na arewacin Najeriya Allah ya albarkace su da hazikan mutane masu dumbin basira da hazaka a dukkan fannoni na rayuwa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng