Sanatoci sun zargi ministocin Buhari 2 da gwamnan CBN da makarkashiyar siyen jirgin yaki

Sanatoci sun zargi ministocin Buhari 2 da gwamnan CBN da makarkashiyar siyen jirgin yaki

Yan majalisar dattijan Najeriya sun zargi ministocin kudade da kuma na tsaro a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari gami da shugaban babban bankin Najeriya na CBN da hada baki wajen fitar da makudan kudaden da suka kai $462 miliyan don siyen jirgin yaki mai saukar angulu.

Yanzu haka dai tuni har majalisar dattijan ta aiki da takardar sammaci zuwa ga jami'an gwamnatin da suka ce suna so su bayyana a gaban su domin bayar da ba'asi kan yadda akayi har hakan ta faru.

Sanatoci sun zargi ministocin Buhari 2 da gwamnan CBN da makarkashiyar siyen jirgin yaki

Sanatoci sun zargi ministocin Buhari 2 da gwamnan CBN da makarkashiyar siyen jirgin yaki

KU KARANTA: PDP ta jajantawa almajiran Zakzaky

Legit.ng ta samu cewa tun farko dai, Sanata Sam Anyanwu na jam'iyyar PDP daga jihar Imo ne dai ya gabatar da kudurin bincikar jami'an a zauren majalisa.

A wani labarin kuma, Shugaban jam'iyyar nan ta Social Democratic Party (SDP), mai ra'ayin 'yan mazan jiya watau Cif Olu Falae a jiya ne yayi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo musamman ma domin ganin yadda za su bullowa hana shugaba Buhari zarcewa a zaben 2019 mai zuwa.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawa, shugaban jam'iyyar ta Social Democratic Party (SDP) na kasa baki daya, Chief Olu Falae ya bayyana cewa a bisa dukkan alamu dai kusan komai baya tafiya yadda ya kamata a kasar nan kuma dole ne ayi wani abu a kai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel