Zaben 2019: Obasanjo ya fara jagorantar shirin karya kashin bayan Shugaba Buhari

Zaben 2019: Obasanjo ya fara jagorantar shirin karya kashin bayan Shugaba Buhari

Shugaban jam'iyyar nan ta Social Democratic Party (SDP), mai ra'ayin 'yan mazan jiya watau Cif Olu Falae a jiya ne yayi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo musamman ma domin ganin yadda za su bullowa hana shugaba Buhari zarcewa a zaben 2019 mai zuwa.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawa, shugaban jam'iyyar ta Social Democratic Party (SDP) na kasa baki daya, Chief Olu Falae ya bayyana cewa a bisa dukkan alamu dai kusan komai baya tafiya yadda ya kamata a kasar nan kuma dole ne ayi wani abu a kai.

Zaben 2019: Obasanjo ya fara jagorantar shirin karya kashin bayan Shugaba Buhari

Zaben 2019: Obasanjo ya fara jagorantar shirin karya kashin bayan Shugaba Buhari

KU KARANTA: An goga mun bakin jini a Najeriya - IBB

Legit.ng ta samu cewa haka zalika ma shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa ya goyi bayan shugaban kasa Buhari ne a zaben 2015 da zummar zai kawo sauyi a kasar amma a cewar sa har yanzu hakan ba ta samu ba don haka ne ma yake so ya canza shi.

A wani labarin kuma, Yan majalisar dattijan Najeriya sun zargi ministocin kudade da kuma na tsaro a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari gami da shugaban babban bankin Najeriya na CBN da hada baki wajen fitar da makudan kudaden da suka kai $462 miliyan don siyen jirgin yaki mai saukar angulu.

Yanzu haka dai tuni har majalisar dattijan ta aiki da takardar sammaci zuwa ga jami'an gwamnatin da suka ce suna so su bayyana a gaban su domin bayar da ba'asi kan yadda akayi har hakan ta faru.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel