Takarar Gwamna 2019: Shehu Sani ya musanta zargin shekewa daga APC zuwa SDP

Takarar Gwamna 2019: Shehu Sani ya musanta zargin shekewa daga APC zuwa SDP

Sanatan al’ummar Kaduna ta tsakiya ya bayyana cewa zai sanar da jama’a a duk lokacin da zai sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyya ta daban, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya musanta jita jitan da ake yadawa na cewa wai ya koma jam’iyyar SDP da nufin taka takarar gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2019, a inuwar jam’iyyar.

KU KARANTA: Daukar dala ba gammo: Ka halasta Luwaɗi da maɗigo a Najeriya – Shugaban kasar Ingila ga Buhari

Sai dai Sanatan yayi amfani ne da kalaman kwallon kafa wajen isar da sakon nasa, inda yace: “Har yanzu ina kungiyar kwallon kafa ta masu tsintsiya, a matsayina na dan wasan gefe, ba dan wasa ba, don haka labarin da ake yadawa na cewa wai na koma kungiyar kwallon kafa ta farar doki ba gaskiya bane.”

Takarar Gwamna 2019: Shehu Sani ya musanta zargin shekewa daga APC zuwa SDP

Sanii

Daga karshe ya karkare bayanin nasa da cewa: “Idan har akwai wani sauyin sheka da zan yi kafin karshen kakar kwallon bana, zan sanar da ku. Nagode.”

Dangantaka dai ta yi tsami ne a tsakanin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai da Sanata Shehu Sani, inda Sanatan ke zargin Gwamnan da girman kai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku Latsa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel