2019: Mutanen da ke shirin fitowa takarar Sanatan Kaduna

2019: Mutanen da ke shirin fitowa takarar Sanatan Kaduna

Yanzu haka an kada gangar zaben 2019 inda manyan 'Yan siyasa su ka fara nuna yadda za ta kasance. Mun kawo maku yadda lissafin siyasar yake a cikin Jihar Kaduna a Arewacin kasar.

Tuni dai har wasu sun nuna shirin su na fitowa takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya wanda hakan barazana ne ga Sanatan mai-ci Shehu Sani. Ga dai jerin masu neman kujerar Sanatan nan:

2019: Mutane 3 da ke shirin fitowa takarar Sanatan Kaduna

Lawal Samaila Yakawada zai fito takarar Sanata

1. Lawal Samaila Yakawada

Yakawada wanda asalin sa 'Dan Giwa ne yana cikin manyan 'Yan siyasa na Jihar Kaduna. Yakawada ya taba rike Sakataren Gwamnati a Kaduna kuma ya nemi Gwamna. Yanzu haka yana cikin manyan masu ba Gwamna Nasir El-Rufai shawara.

KU KARANTA: Bola Tinubu ya bayyana matsalar da Buhari yake fuskanta

2. Uba Sani

Dr. Uba Sani wanda yana cikin manyan na-hannun daman Gwamna Nasir El-Rufai yana cikin masu harin kujerar Sanata Shehu Sani. Sani dai zai yi kokarin ganin karshen Shehu Sani wanda yake yin fito-na-fito da mai girma Gwamnan Jihar.

3. Shamsu Giwa

Arch. Giwa wanda ya fito daga Yanki daya da Lawal Samaila Yakawada yana cikin masu neman zuwa Majalisar Dattawa a 2019. Shamsu Giwa ya taba tsayawa takara a Karamar Hukumar sa a baya kuma ya dade yana goyon bayan Shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel