Kwankwaso yayi farin cikin bayan Kotun koli ta ba shi gaskiya a game da zaben 2015

Kwankwaso yayi farin cikin bayan Kotun koli ta ba shi gaskiya a game da zaben 2015

- Kwankwaso ya kara samun nasara game da zaben sa na 2014 a Kotu

- Ana kalubalantar yadda Kwankwaso ya samu tikitin Sanata a APC

- A baya an shiga Kotu da tsohon Gwamnan na Kano kan kujerar sa

Jiya ne Tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana murnar sa bayan da babban Kotun Najeriya ta kammala shari'a game da kujerar da yake kai na Sanatan Kano ta tsakiya. Yanzu Kotu tayi watsi da karan da ke gaban ta.

Kwankwaso yayi farin cikin bayan Kotun koli ta ba shi gaskiya a game da zaben 2015

Kotun Koli tayi fatali da karar da aka kai Kwankwaso

An maka Rabiu Kwankwaso a Kotu inda ake kalubalantar tikitin da ya samu na Sanata a karkashin Jam'iyyar APC. Masu karar su na ganin hanyar da Tsohon Gwamnan ya bi wajen lashe zaben fitar da gwani ya sabawa ka'ida.

KU KARANTA: Jama'a sun tarbi Kwankwaso a Garin Shugaban kasa

Sai dai Kotu ta bayyana cewa babu wata matsala a zaben da aka yi na kujerar Sanatan a APC a 2014. 'Dan Majalisar ya ji dadin yadda shari'ar ta kare inda yace hakan ya sa ya kara samun kwarin-gwiwa kan bangaren shari'a a Kasar.

A 2014 dai Sanatan yayi takarar tikitin Shugaban kasa a karkashin APC inda ya zo na biyu bayan Shugaban kasa Buhari. Daga nan ne ya koma ya nemi takarar Sanatan inda shi kuma Rochas Okorocha kuma ya koma kujerar Gwamnan sa.

Dubi yadda Sanatan ya karbu a Garin Daura a makon nan

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel