Majalisar Dattawa ta tabbatar da amincin mukaman shugaban NHRC da shugaban NERC

Majalisar Dattawa ta tabbatar da amincin mukaman shugaban NHRC da shugaban NERC

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne majalisar dattawa ta tabbatar da amincewar ta dagane da nadin mukami na babban sakataren hukumar kare hakkin dan Adam ta NHRC (National Human Rights Commission), Mr Anthony Ojukwu.

Majalisar ta kuma tabbatar amincewar ta ga mukamin Farfesa James Momoh, a matsayin shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta NERC (Nigerian Electricity Regulatory Commission).

Majalisar Dattawa ta tabbatar da amincin mukaman shugaban NHRC da shugaban NERC

Majalisar Dattawa ta tabbatar da amincin mukaman shugaban NHRC da shugaban NERC

Legit.ng ta fahimci cewa, tabbatuwar Ojukwu ta biyo bayan binciken kwamitin majalisar akan harkokin shari'a da kuma kare hakkin dan Adam.

Da yake gabatar da rahoton sa, Mataimakin shugaban kwamitin Sanata Babajide Omoworare ya bayyana cewa, binciken da suka gudanar ya tabbatar da aminci da kuma cancantar Ojukwu na rike mukamin babban sakataren hukumar NHRC.

KARANTA KUMA: Ababe 8 da kwaskwarimar Masallacin Harami na Makkah ta kunsa

Hakazalika, tabbatar da Momoh ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin wutar lantarki da kuma masana'antun ƙera ƙarafa da sanadin shugaban sa, Sanata Enyinnaya Abaribe.

A cikin jawaban sa, mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu, ya taya murna ga wannan sabbin jagorori biyu da suka cancanci mukamai, inda ya kuma gargade su akan zage dantsen su wajen fuskantar duk wani kalubale a yayin gudanar da aikin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel