Tsaka mai wuya: Yadda aka hallaka wani matashi mai shekaru 20 a gidan wani fitaccen dan siyasa

Tsaka mai wuya: Yadda aka hallaka wani matashi mai shekaru 20 a gidan wani fitaccen dan siyasa

Rundunar Yansandan jihar Borno ta sanar da kisan wani matashi mai shekaru 20, Maina Mustapha a gidan wani hamshakin dan siyasar jihar, Grema Terab, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Kwamishinan Yansandan jihar, Damian Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Talata 17 ga watan Afrilu, inda yace a yanzu haka sun kama mutane 24 dangane da binciken yadda aka kashe yaron, kuma su waye.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a Benuwe, sun kashe Dagacix

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamishina Damian yana cewa sun gano gawar Maina wanda yake sana’ar walda ne a gidan Grema bayan samun rahoton kisan, inda yace sai da suka shawarci Gream cewar kada ya kuskura ya shirya gangamin siyasa a gidansa, amma yayi kunnen uwar shegu.

“Bayan Grema ya aiko mana da wasikar neman izini, sai muka shawarce shi da kada ya hada gangamin siyasa a gidansa, ya kai taronsa zuwa filin wasa, ko kuma Otal, ko kuma dai wani budadden waje, don ta haka ne kadai zamu iya samar da tsaron da ya dace a taron. Amma yaki, yayi gaban kansa, inda a yayin taron aka caka ma Maina wuka.” Inji shi.

Kwamishinan ya cigaba da fadin samun labarin gano gawar yaron a gidansa ke da wuya, sai Grema ya ranta ana kare, inda a yanzu haka ya buya, bayan rundunar Yansandan jihar ta aika masa da sammaci.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jihar Borno ta yi caraf da wata yar karamar yarinya mai shekaru 13, da Boko Haram suka yi mata jigida da Bama Bamai da nufin ta kai harin kunar bakin wake a garin Maiduguri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel