An sake kwatawa: Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a Benuwe, sun kashe Dagaci

An sake kwatawa: Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a Benuwe, sun kashe Dagaci

Tabarbarewa al’amuran tsaro a jihar Benuwe na cigaba da ta’azzara, inda a ranar Talata 17 ga watan Afrilu wasu yan bindiga suka kai hari wani kauyen jihar, inda suka bindige Dagacin kauyen, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yan bindigar sun kashe Iyongovihi Ninge, dagacin kauyen Ukemberagya da Tsarev, inda yan kabilar Chembe suka fi yawa, a cikin karamar hukumar Logo na jihar Benuwe.

KU KARANTA: Rikicin jihar Benuwe: Sojojin Najeriya sun yi arangama da makiyaya, mutane 4 sun rasa rayuwarsu

Wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyarmu cewar Dagacin ya tafi gonarsa ne a ranar Talata da nufin duba aikin da yasa wasu matasa su yi masa na gyaran gona, domin shirin noman damina dake karatowa, isarsa gonar keda wuya, sai yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka dira gonar.

Hangen makiyayan yasa matasan dake aiki a gonar suka ranta ana kare don tseratar da ransu, sai dai ko kafin Dagacin ya ankara, har yan bindigar sun dirka masa harsashi a baya, nan take Dagacin ya fadi matacce, ba ko shuruwa.

Shugaban karamar hukumar Logo ya bayyana ma majiyarmu cewar ya samu rahoton kisan Dagacin, inda yace yan bindigar sun fatattaki manoma daga gonakinsu, suka mamaye gonakan da shanunsu.

Sai dai kwamishinan Yansandan jihar, Fatai Owoseni yace har zuwa yanzu bai samu rahoton kisan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel