Tinubu ya yi magana a kan takarar Buhari, ya yi bayanin matsalar da suke fuskanta

Tinubu ya yi magana a kan takarar Buhari, ya yi bayanin matsalar da suke fuskanta

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce abinda gwamnatin jam'iyyar APC ta yi cikin shekaru uku, PDP ko kwatankwacin sa bata yi a tsawon shekaru 16 da tayi tana mulki.

Tinubu ya bayyana cewar babbar matsalar da suke fuskanta, ita ce ta kokarin tsaftace dagwalon datti da mulkin jam'iyyar PDP ya bari a Najeriya.

A cewar Tinubu, jam'iyyar APC tayi hannun riga da jam'iyyar PDP, wacce ya ce tafi kwarewa a bangaren cikar burin jagororin ta a kan na kasa.

Tinubu ya yi magana a kan takarar Buhari, ya yi bayanin matsalar da suke fuskanta

Tinubu da Buhari

Tinubu ya ce yanai matukar takaicin yadda gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaba Buhari ta shafe lokaci domin kawo gyara da tsafta daga barna da datti da gwamnatin PDP ta haifar a Najeriya.

Kazalika ya ce lokaci na zuwa da gwamnatin jam'iyyar APC zata mayar da hankali ne kawai wajen manyan aiyuka, lokacin ta gama saita al'amuran Najeriya a kan hanyar cigaba.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Wasu 'yan majalisar wakilai biyu sun jefar da PDP, sun canja sheka

Tinubu na wadannan kalamai ne a matsayin babban bako a wurin taron cika shekaru 35 da mutuwar Mallam Aminu Kano.

An raba jawabin na Tinubu ga manema labarai kamar yadda gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya karanta a madadin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel