Rikicin jihar Benuwe: Sojojin Najeriya sun yi arangama da makiyaya, mutane 4 sun rasa rayuwarsu

Rikicin jihar Benuwe: Sojojin Najeriya sun yi arangama da makiyaya, mutane 4 sun rasa rayuwarsu

Rundunar Sojin kasa ta Najeriya ta fafata da wasu yan bindiga makiyaya a jihar Benuwe, inda Sojoji suka hallaka makiyaya guda hudu, kamar yadda jaridar ‘The Nation’ ta ruwaito.

Kaakakin rundunar, Birgediya Texas Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Talata 17 ga watan Afrilu, inda yace bayan makiyayan da Sojoji suka kashe, sauran makiyayan sun ranta ana kare sakamakon ruwan wuta da suka sha.

KU KARANTA: Ka halasta Luwaɗi da maɗigo a Najeriya – Shugaban kasar Ingila ga Buhari R

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana cewa: “Sojojin bataliya ta 72 dake jihar Benuwe karkashin aiki na musamman mai taken ‘Operation MESA’ sun yi arangama da makiyaya yan bindiga guda 20 a kauyen Yogbo na karamar hukumar Guma, inda suka kashe guda hudu, yayin da sauran suka tsere.

“Sojoji sun samu nasarar kwato makaman da suka hada da bindigu kirar AK47 guda hudu, da kuma alburusai da dama, daban daban. Don haka rundunar Sojan kasa na jaddada manufarta na kakkabe ayyukan miyagun mutane daga Najeriya gaba daya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Yan bindiga sun bindige yansanda guda shidd a jihar Benuwe, bayan wani harin kwantan bauna da suka kai musu a ranar Asabar 14 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel