Sabon Sanatan nan mai son rawa zai takarar gwamna a jam'iyyar ta PDP

Sabon Sanatan nan mai son rawa zai takarar gwamna a jam'iyyar ta PDP

- Sanata Adeleke zaiyi takarar gwamna a 2019 a jiharsa ta Osun

- An san Sanatan da rawa kamar dan yaro bayan da yaci zabe a bara

- Sanatan ya rattabawa uwar jam'iyya wasika kan aniyarsa a 2018 dinnan

Sabon Sanatan nan mai son rawa zai takarar gwamna a jam'iyyarsa ta PDP
Sabon Sanatan nan mai son rawa zai takarar gwamna a jam'iyyarsa ta PDP

Sanata Ademola Adeleke, sanata mai son rawa a bainar jama'a, wanda ya ja hankalin kasar nan a bara jim kadan bayan cin zabensa, ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamnan jiharsa ta Osun a zaben da za'a yi a bana a Satumba.

Yayansa ne dai ya rasu a kujerar Sanatan Osun West a Arilun bara, inda aka yi zaben maye gurbi yaci a karkashin PDP, duk da da dan APC ne.

Ya canja jam'iyyar ne kwanaki kadan kafin ayii zaben, domin da yana APC ne.

DUBA WANNAN: Batutuwa da shugaba Buhari ya tauna a Ingila

A watan Satumba ne dai za'ayi zaben jihar, inda yace wa jam'iyyarsa a jijar ta bashi takara domin ya hado kan 'yan jihar su kori APC daga jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel