Karyar rashin aure: An yankewa magidanci daurin shekaru uku a gidan yari

Karyar rashin aure: An yankewa magidanci daurin shekaru uku a gidan yari

Wata kotu dake sauraron korafe-korafe na musamman ta yankewa wani magidanci dake burin samun bizar fita Turai hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bayan samun sa da laifin yin 'yar boka, wato karya.

Hukumar yaki da rashawa da aikata miyagun laifuka (ICPC) ce ta gurfanar da mutumin, Kolawale Viyon, bayan ya yi karyar bashi da aure a takardun da ya cike na neman bizar tafiya kasar Ingila.

Karyar rashin aure: An yankewa magidanci daurin shekaru uku a gidan yari

Karyar rashin aure: An yankewa magidanci daurin shekaru uku a gidan yari

Alkalin kotun Mojisola Dada ya ce wanda ake gurfanar din ya amsa lifinsa. Kazalika, alkalin ya bashi zabin biyan tarar N300,000 cikin sa'o'i 24 ko kuma a tisa keyar sa zuwa gidan yari bayan karewar wa'adin.

DUBA WANNAN: An gano gawarwakin 'yan sanda 6 da aka kashe jiya a Benuwe

Saidai nan take lauya mai kare wanda ake kara ya ce a shirye su ke su biya adadin kudin.

Jami'an ofishin jakadancin kasar Ingila ne suka mika Mista Viyon hannun hukumar ICPC a shekarar 2016 saboda bayar da bayanan karya a takardun da ya cike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel