Kididdigar ta'adin gobara a Legas: Rayuka da biliyoyin da aka yi asara

Kididdigar ta'adin gobara a Legas: Rayuka da biliyoyin da aka yi asara

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewar a kalla mutane 84 da dukiyoyin biliyan N12.8bn aka yi asara cikin shekarar da ta gabata sakamakon gobara.

Kwamishinan aiyukan na musamman a jihar, Mista Oluseye Oladejo, ne ya fitar da wadannan alkaluma a jiya Litinin yayin shaidawa manema labarai nasarar da ma'aikatar sa ta samu daga watan Mayu zuwa Afrilu na shekarar nan, 2018.

Kididdigar ta'adin gobara a Legas: Rayuka da biliyoyin da aka yi asara

Jami'an kashe gobara

A cewar sa, anyi nasarar kubutar da mutane 333 da gobara ta shafa yayin da aka samu gawarwakin mutane 84 a wuri daban-daban da gobara ta taba tashi.

DUBA WANNAN: Jirgin yakin hukumar soji MI-35M ya yi ruwan nakiyoyi a kan motocin 'yan Boko Haram

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin jihar Legas ta gyara cibiyoyin samar da ruwa domin kashe gobara a cibiyoyi 225 tare da samar da wasu 50 sabbi a sassa daban-daban dake jihar.

Domin kiyaye afkuwar hadurra da rage cunkoson ababen hawa, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar zata fara janye duk wasu matatun ababen hawa da aka jibge a gefen titunan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel