Badakalar dala miliyan 462: Majalisar Dattawa ta bukaci Ministocin Buhari da gwamnan CBN su gurfana a gabanta

Badakalar dala miliyan 462: Majalisar Dattawa ta bukaci Ministocin Buhari da gwamnan CBN su gurfana a gabanta

A ranar Talata 17 ga watan Afrilu ne majalisar dattawa ta yanke shawarar neman minister kudi, Kemi Adeosun, ministan tsaro Mansur Dan Ali tare da gwamnan babban bankin Najeriya,CBN, Godwin Emefiele da su gurfana a gabansu don amsa tambayoyi game da zare dala miliyan dari hudu da sittin da biyu, 462 daga lalitar gwamnati.

Daily Nigerian ta ruwaito majalisa ta zargi manyan jami’an gwamnatin Buhari da zare kudin daga baitil malin gwamnati ba tare da bin ka’ida ba, musamman ka’idar da tace lallai sai shugaban kasa ya nemi izinin majalisa kafin ya cire irin wadannan makudan kudade.

KU KARANTA: Ga koshi ga kwanar yunwa: An hallaka wani matashi bayan ya ciyo naira miliyan 11 a caca

Sanata Samuel Anyanwu na jam’iyyar PDP daga jihar Imo ne ya janyo hankalin majalisar game da wannan badakala, inda yace ya samu labari daga majiya mai tushe cewa gwamnati ta yi amfani da kudin ne wajen siyan jiragen sama masu tashin angulu daga wata kamfanin kasar Amurka.

Badakalar dala miliyan 462: Majalisar Dattawa ta bukaci Ministocin Buhari da gwamnan CBN su gurfana a gabanta

Majalisa

Sanatan ya bayyana cewa sashi na 80 (2) da (3) na kundin tsarin mulki sun haramta ma gwamnatin tarayya cire makudan kudade daga lalitar gwamnati ba tare da izinin majalisa ba, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

“Ina da tabbacin gwamnati bata taba kawo wannan bukata a gabanmu ba, don haka nake so mu bi diddigin wannan badakala, ta hanyar gayyatar wadanda abin ya shafa, ministan kudi, ministan tsaro da gwamnan babban bankin Najeriya.” Inji shi.

Daga nan sai mataimakin shugaban majalisa dattawa, Ike Ekweremadu ya nemi jin ta bakin sauran yan majalisun, inda dukkaninsu suka amince a gayyato manyan jami’an gwamnatn shugaban kasa Muhammadu Buhari don amsa tambayoyi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel