Dalilin da ya sanya muka kama ‘Yan Shi’a 115 cikin masu zanga-zanga - ‘Yan Sanda

Dalilin da ya sanya muka kama ‘Yan Shi’a 115 cikin masu zanga-zanga - ‘Yan Sanda

- Hukumar ‘Yan Sanda na birnin tarayya sun bayyana cewa, sunyi arangama tsakaninsu da ‘Yan Shi’ar ne a ranar Litnin bayan sun fito suna zanga-zangar a saki shugabansu Ibrahim El-Zakzaky

- ‘Yan Sandan wadanda suka fita aikin a Unity Park da Transcorp Hilton Hotel sun watsawa masu zanga-zangar hodar ibilis ne don su koresu daga cigaba da aiwatar da zanga-zangar

- Hukumar ‘Yan Sandan na birnin tarayya tace sun kama mutane 115 na kungiyar, sakamakon sun fara kaiwa mutanen gari da ababen hawa na mutane hari

Hukumar ‘Yan Sanda na birnin tarayya sun bayyana cewa sunyi arangama tsakaninsu da ‘Yan Shi’ar ne a ranar Litnin, 16 ga watan Afirilu, bayan sun fito suna zanga-zangar a saki shugabansu Ibrahim El-Zakzaky.

‘Yan Sandan wadanda suka fita aikin a Unity Park da Transcorp Hilton Hotel sun watsawa masu zanga-zangar hodar ibilis ne don su koresu daga cigaba da aiwatar da zanga-zangar, wanda hakan yasa suka rinka jifar motocin ‘Yan Sanda da duwatsu.

Dalilin da ya sanya muka kama ‘Yan Shi’a 115 cikin masu zanga-zanga - ‘Yan Sanda

Dalilin da ya sanya muka kama ‘Yan Shi’a 115 cikin masu zanga-zanga - ‘Yan Sanda

Hukumar ‘Yan Sandan na birnin tarayya tace sun kama mutane 115 na kungiyar, sakamakon harin da suka fara kaiwa mutanen gari da ababen hawa suna fashe gilassai na motocin mutane, wadanda ke yankin da lamarin ke aukuwa, kuma sun kawo tsayuwar kasuwanci da cushewar hanyoyi a yankin.

KU KARANTA KUMA: Nyass ba Allah ba ne, masu danganta shi da Allah sun kafirta - Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir

Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da huddodin jama’a na jihar Anjuguri Manzah, ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike a kan lamarin, saboda anjiwa jami’an ‘Yan Sandan 22 rauni a lokacin da suke zanga-zangar, yace kuma wadanda aka kama za’a gurfanar dasu a gaban kotu da zarar an kamala bincike.

‘Yan Sandan sunce anyi sa’a tinda ba’a rasa rai ko guda ba, a zanga-zangar data kare da rikici, sakamakon jami’an da aka tura aikin sunyi shi ne akan kwarewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel