Sai na zama Shugaban kasa a Najeriya - Fasto Bakare

Sai na zama Shugaban kasa a Najeriya - Fasto Bakare

- Fasto Tunde Bakare shugaban cocin Latter Rain Assembly ya bayyan cewa sai ya zama shugaban kasa a Najeriya

- Bakare ya bayyana hakane a ranar Lahadi lokacin da shugaban watsa labarai na Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya kai masa ziyar cocinsa a matsayin babban bako

- Malamin Kiristancin yace Sowore ma zai jagoranci Najeriya shima

Fasto Tunde Bakare shugaban cocin Latter Rain Assembly ya bayyan cewa sai ya zama shugaban kasa a Najeriya.

Bakare ya bayyana hakane a ranar Lahadi 15 ga watan Afirilu, lokacin da shugaban watsa labarai na Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya kai ziyara a cocinsa, a matsayin babban bako.

Sai na zama Shugaban kasa a Najeriya - Fasto Bakare

Sai na zama Shugaban kasa a Najeriya - Fasto Bakare

Legit.ng ta ruwaito cewa Malamin Kiristancin yace dashi da Sowore zasu jagoranci Najeriya, saboda dukansu hankalinsu na kan kujerar shugaban kasa a Najeriya saboda haka sai sun mulki kasar.

KU KARANTA KUMA: Nyass ba Allah ba ne, masu danganta shi da Allah sun kafirta - Inji Sheikh Sani Yahaya Jingir

Bakare wanda dama tun a shekarar 2011 sunyi takara tare da shugaba Buhari a karkashin jam’iyyar CPC, duk da dai basuyi nasara ba a lokacin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel