Yawaitar kashe-kashe a Zamfara: Na mika wa Allah, zan dauki nauyin yin addu'o'i - Gwamna Yari

Yawaitar kashe-kashe a Zamfara: Na mika wa Allah, zan dauki nauyin yin addu'o'i - Gwamna Yari

Gwamnatin jihar Zamfara zata shirya addu'a na musamman don rokon Allah ya kawo sauki kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye jihar. Wani jami'in gwamnatin, Malam Aminu Danjibga ya shaidawa manema labarai a Gusau cewa za'a fara adduo'in daga yau har zuwa karshen watan Mayu.

Danjigba wanda shine Ciyaman din karamar kwamitin wa'azi da addu'o'i na kwamitin shirya bukin cikar gwamna Yari shekaru 7 kan mulki yace addu'o'in na daga cikin ababen da za'a gudanar don murnar cikar gwamnatin shekara 7 kan mulki.

Za muyi addu'a na musamman saboda kashe-kashen da afkuwa a Zamfara - Gwamna Yari

Za muyi addu'a na musamman saboda kashe-kashen da afkuwa a Zamfara - Gwamna Yari

Wasu daga cikin kalamansa, "Mun shirya wa'azi da addu'o'i wanda za'a rika gudanarwa daga yau har karshen watan Mayu saboda bikin cika shekaru 7 a mulki na wannan gwamnatin.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe mutum biyu a wajen wani biki

"Kamar yadda ka sani, jihar mu na fuskatan kallubale na tsaro; Yan daba na kai hare-hare a garuwa suna kashe al'umma kuma abin yana matukar damun mu.

"Duk da kokarin gwamnati da jami'an tsaro, har yanzu matsalar bata gushe ba; a matsayin mu na musulmai addu'a itace babban makamin mu kan duk wata matsala da ke adabar mu."

Danjibga kuma ya ce za'a gudanar da addu'o'i a masallatan Juma'a a dukkan fadin jihar, sannan kuma za'a shirya wasu addu'o'in a gudumomin mulki 17 da ke jihar.

Ya kuma ce za'a gayyato mallamai wanda zasuyi saukan karatun Kur'ani mai girma daga kananan hukumomi 14 da ke jihar kuma suyi addu'a ga Allah ya kawo karshen fitinar rashin tsaron da ke adabar jihar.

Danjibga, wanda shine shugaban kwamitin harkokin addinin na majalisar jihar, yayi kira ga dukkan al'ummar jihar su rika yin addu'o'i na musamman saboda Allah ya kawo karshen fitinar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel