Da duminsa: An nada shahrarren lauya, Festus Keyamo, a matsayin kakakin yakin neman zaben Buhari na 2019

Da duminsa: An nada shahrarren lauya, Festus Keyamo, a matsayin kakakin yakin neman zaben Buhari na 2019

Kungiyar yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari a 2019 karkashin jagorancin ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ta nada shahrarren lauya, Mr Festus Keyamo SAN, a matsayin kakakin yakin neman zaben Buhari 2019.

Ga dukkan alamu dai an fara shirya-shiryen fara yakin neman zaben 2019. Yayinda shugabannin jam'iyyar PDP ke kai ziyaran tattaunawa da IBB, kungiyar yakin neman zaben shugaba Buhari ta nada Barista Festus Keyamo, a matsayin kakakinta.

Wannan sanarwa ya fito ne a wani wasika da ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya rubutawa lauyan a jiya Litinin, 16 ga watan Afrilu 2018.

Da duminsa: An nada shahrarren lauya, Festus Keyamo, a matsayin kakakin yakin neman zaben Buhari na 2019

Da duminsa: An nada shahrarren lauya, Festus Keyamo, a matsayin kakakin yakin neman zaben Buhari na 2019

Wasikar tace: "Ina matukar farin cikin sanar da kai cewa kungiyar yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari ta nada ka diraktan sadarwa na zaben shugabancin kasan 2019/

Kamar yadda ka sani, shugaba Muhammadu Buhari ya alanta niyyar sake takara a jam'iyyarmu ta APC. An nada ka ne domin ka taimaka wajen nasara a zaben fidda gwani kafin 2019.

A matsayinka za ka kasance kakakin yakin neman zaben lokacin fidda gwani da kuma yakin neman zaben shugaban kasa a 2019."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel