Majalisa ta bukaci Emefiele, Adeosun da wasu su bayyana kan batun sayar helikwafta na $462m

Majalisa ta bukaci Emefiele, Adeosun da wasu su bayyana kan batun sayar helikwafta na $462m

Majalisar dattawa ta umurci ministan kudi, Mrs Kemi Adeosun da ministan tsaro, Brig. janar Mansur Dan-Ali (murabus) da gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Godwin Emefiele su gurfana gaban majalisar don amsa tambayoyi kan kudi $462 da aka ce an cire daga asusun haraji na gwamnatin tarayya.

An ce an cire kudin ne saboda a biya wata kamfanin kasar Amurka wadda ta sayar wa Najeriya jirage kirar helikwafta inda kuma akace da amincewar majalisar ne aka fitar da kudaden.

Majalisa ta bukaci Emefiele, Adeosun da wasu su bayyana kan batun sayar helikwafta na $462m

Majalisa ta bukaci Emefiele, Adeosun da wasu su bayyana kan batun sayar helikwafta na $462m

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: An nada Festus Keyamo diraktan sadarwa na kamfen din Buhari na zaben 2019

Sanata Samuel Anyanwu daga jihar Imo ne ya gabatar da korafin a gaban majalisa a yau Talata inda yace an sabawa sashi na 80(2) da (3) na kundin tsarin mulki na 1999.

Anyanwu yace babu lokacin da aka tura takardan neman amincewar majalisar kan batun cire kudin daga asusun gwamnatin tarayya, saboda hakan yana son majalisa ta bincika yadda aka cire kudaden daga asusun.

Mataimakin shugaba majalisa, Ike Ekweremadu ya gabatar da batun a gaban majalisa inda dukkansu suka amince a bincika batun, hakan yasa Ekweremadu ya mika binciken ga kwamitin daidaito kuma yace su gayyaci ministocin da gwamnan babban bankin kasa (CBN).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel