Babbar Magana: Ma'aikatan Lafiya za su shiga Yajin Aiki na sai Mama ta gani

Babbar Magana: Ma'aikatan Lafiya za su shiga Yajin Aiki na sai Mama ta gani

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Premium Times sun bayyana cewa, a daren ranar Talata ta yau ne kungiyar ma'aikatan lafiya ta JOHESU, (Joint Health Sector Unions) za ta afka yajin aikin gadan-gadan na sai Mama ta gani a gaba daya ma'aikatun lafiya na kasar nan.

Mataimakin shugaban wannan kungiya Ogbonna Chimmela, shine ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata yayin ganawa da manema labarai.

Mista Chimela yake cewa, yajin aikin zai dakile dukkanin ma'aikatun lafiya na gwamnatin tarayya, wanda idan gwamnatin ta kyale yajin aiki ya ci gaba bayan makonni biyu na jihohi da kananan hukumomin za su biyo baya.

Babbar Magana: Ma'aikatan Lafiya za su shiga Yajin Aiki na sai Mama ta gani

Babbar Magana: Ma'aikatan Lafiya za su shiga Yajin Aiki na sai Mama ta gani

Legit.ng ta fahimci cewa, mambobin kungiyar JOHESU ta hadar da ungozomai, mataimakan likitoci da kuma masu bayar da magani.

A watan Satumba na shekarar da ta gabata ne kungiyar JOHESU ta shiga yajin aiki domin zanga-zanga da suka shafi wasu bukatu musamman na albashin mambobin ta, wanda wannan lamari ya kawo tsaiko a harkokin kiwon lafiya a kasar nan.

KARANTA KUMA: Shehu Inyass ya bayar da gudunmuwa ta bunkasar addinin Musulunci a duniya - Buhari

Wannan kungiya dai za ta shiga yajin aikin ne a sakamakon rashin ciki alkawarin gwamnatin tarayya dangane da yarjejeniyar da ta kulla watanni shidda da suke gabata.

Gwamnatin tarayya ta sha alwashin cika alkawurran ne cikin makonni biyar, sai dai cikin mamaki na kungiyar yau watanni shida kenan ba bu amo bare labari.

Wannan lamari ya sanya kungiyar za ta shiga yajin aikin a daren yau Talata sakamakon shi kadai ne yaren da gwamatin tarayya ke fuskanta wajen biyan bukatun al'ummarta kamar yadda kungiyar ta bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel